Mahaman Kanta ya sami lambar yabo | Zamantakewa | DW | 04.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Mahaman Kanta ya sami lambar yabo

Gwamnatin Nijar ta bai wa Mahaman Kanta wakilin DW lambar yabo saboda kwazon da ya nuna a kan aikinsa wajen tabbatar da dimokaradiyya albarkacin bikin zagayowar cikar shekaru 56 da kasar ta samu 'yancin kai.

Mahaman Kanta daya daga cikin dadaddun wakilan DW Hausa, gwamnatin ta Nijar ta karramashi da lambar girma ta kasa saboda kokarin da ya bayar a hanyar aikinsa na jarida wajen ci gaban dimokaradiyya a Nijar. Wannan shi ne karo na farko da wani dan jarida da ke yi wa wata kafar jarida ta waje aiki ya sami irin wannan lambar yabo. An dai bayyana sunan Kanta a cikin jerin sunayen wadanda aka bai wa lambar a ranar uku ga watan Augusta, ranar bikin samin 'yancin kai na kasar ta Nijar, kuma sai a nan gaba ne za a kaddamar da bikin mika lambar yabon ga wadanda aka bayyana sunayensu.

Thomas Mösch shugaban sashen Hausa ya yi kyakkyawan yabo ga Kanta

Korrespondenten von DW Haussa im Niger

Daga hannu hagu zuwa na dama Mahaman Kanta shi ne na uku

Mahaman Kanta yana aiki a matsayin wakilin DW tun shekaru 25 da suka wuce, kana kuma ya rika gudanar da aikinsa cike da kwazo da himma. A lokacin mulkin soji Mahaman Kanta ya fuskanci kalubale amma duk da haka bai nuna tsoro ba wajen gudanar da aikinsa a kan turbar da ta dace ta jarida, kamar yadda shugaban sashen Hausa Thomas Mösch ya bayyana.

Wanda ya ce har kullum yakan ci gaba da samun horo ta fannin sabbin fusa'o'i na zamani, kuma tun a lokacin da sauran wakilai na DW suke samun matsala wajen aiko da sakwanninsu da kuma sauti ta hanyar intanet Kanta mai shekaru 60 da haifuwa shi ya riga ya kware a kan aiko sakwannin ta intanet da kuma sauti mai inganci.

Shugaban sashen Hausa Thomas Mösch ya yi misali da Mahaman Kanta da cewar wani mutum ne mai kyakkyawan hali da nuna so da kauna ga sauran abokanan aikinsa. A yanzu yana aiki tare da sauran wakilan DW Hausa guda shidda a Nijar wadanda suke daukarsa tamkar uba, wanda ya kwashe dogon lokaci yana ba da kyawawan shawarwari a garesu domin su kara gyara aikinsu, musamman ga matasan da ya rika bai wa kwarin gwiwa na yin aiki da sabbin fusa'o'i na zamani na intanet. Domin kara samun fahimtar juna tsakanin wakilan, Mahaman Kanta ya kirkiro da wata haduwa ta wakilan DW inda suke tattaunawa lokaci zuwa lokaci a kan aikinsu.

Ministan sadarwa na Nijar Yahouza Sadissou shi ne ya ba da shawara ga gwamnatin don karrama Kanta

DW im Niger Yahouza Sadissou Mabobi

Yahouza Sadissou Mabobi tsohon minista yada labarai na Nijar

Gwamntin ta Nijar dai ta bai wa Kanta wannan lambar yabo ne a sakamakon gudunmowar da ya bayar wajen habaka dimokaradiyya. Karramawar ta samo asali ne tun lokacin da Yahouza Sadssou yana rike da mukamin ministan yada labarai na Nijar, wanda shi ya ba da wannan shawara ga gwamnatin, saboda abin da ya kira irin jan namijin kokarin da Kanta ya bayar a fannin ci gaban dimokaradiyya da ci gaban al'umma. Yahouza Sadissou dai shi ma tsohon ma'aikaci ne na DW kuma a yanzu yana rike da mukamin ministan sadarwa na Nijar.