Mahamadou Tukur mai wasan barkwanci a Nijar | Himma dai Matasa | DW | 10.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Mahamadou Tukur mai wasan barkwanci a Nijar

A Jihar Gaya ta Jamhuriyar Niger wani matashi mai suna Mahamadou Tukur Yakuba ya dukufa wajen samar da zaman lafiya tsakanin kabilun kasar ta hanyar gudanar da wasan kwaikwayo na barkwanci

Junge Fulani Männer beim Nomadenfest Cure Salee im Niger

Shi dai Mahamadou Tukur Yakuba matashi mai shekaru 36 wanda ya kasance fitace a fannin wasanin barkwanci na ban daria tsakanin kabilu daban daban na Kasar Niger, abin da ya kai shi ga kasancewa a matsayin na farko a gasar tabbasantaka ta Nijar a shekara ta 2014. A cikin hirar da tashar DW ta yi da shi Tukur ya bayyana cewa ya saka kansa cikin wannan sana'a domin kara karfafa dangon zumuncin da dama ke da akwai tsakanin kabilun kasar Nijar, inda yake amfani da illahirin harsunan kabilun kasar wajen fadakar da al'umma da nishadantar da su.


To sai dai Oumarou Toudu wanda yake ubangida ga Mahamadou Tukur ya bayyana fatansa na ganin gwamnati ta mayar da hankali sosai kan 'yan wasan kwaikwayo ta hanyar taimaka masu a cikin aikinsu ta la'akari da irin taimakon da suke bayarwa ta hanyar amfani da basirarsu wajen isar da sakonnin zaman lafiya a tsakanin al'umma.