Mahamadou Issoufou ya tattauna da dalibai | Labarai | DW | 16.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahamadou Issoufou ya tattauna da dalibai

Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya gana da wakilan kungiyar dalibai bayan zanga-zangar da suka yi a farkon wannan mako wanda a ciki aka samu asara rai.

Babban magatagarda na kungiyar daliban Ousseini Sambo ya ce sun tattauna da shugaba Issoufou wanda ya dauki alkawarin sake bude tattaunawa tsakanin daliban da gwamnatin,tare kuma da cewar za a dauki mataki na hukunta wadanda aka samu da laifi wajen aikata ta'adi a bangaran jami'an tsaro da ma daliban a lokacin zanga-zangar.Yanzu haka kotu ta salami  wasu daliban 83 wadanda aka kama bayan tashin hankali,sai dai har yanzu  ana ci gaba da tsare  wasu shugabannin kungiyar daliban a gidan kurkuku.