1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Mahaifiyar Navalny ta yi tozali da gawarsa

February 22, 2024

Mahaifiyar Alexei Navalny ta yi tozali da gawar mamacin kwanaki shida bayan rasuwarsa a gidan kurkukun yankin Artic mai tsananin sanyi da ke wajen birnin Moscow.

https://p.dw.com/p/4cm3B
Weltweite Anteilnahme nach Tod von Navalny
Hoto: Liesa Johannssen/REUTERS

Bayan share kwanaki tana jiran izini daga fadar gwamnatin Poutine, mahaifiyar jagoran adawar Rasha Alexei Navalny ta ziyarci gawarsa a ranar Alhami 22.02.2024 a wani gidan ajiye gawarwaki.

Sai dai cikin bacin rai mahaifiyar ta Navalny ta ce ta fuskanci barazana daga mahukuntan Moscow tare yi mata matsin lamaba domin suna son yi masa jana'iza a asirce.

Mme Lioudmila Navalnaïa ta kuma ce masu bincike kan gawar ta Navalny sun riga sun tabbatar da dalilan mutuwar madugun adawan sannan kuma za su mika takardun binciken ga kotu.

Tuni dai makusantan Navalny da ya share shekaru uku a gidan kurkuku suka zargi gwamnatin Rasha da yunkurin boye hojjojin a kan musabbabin mutuwar jagoran adawar da ke zama babban mai kalubalantar shugaba Vladimir Poutine.