Magoya bayan Mahaman Ousmane a Nijar sun kafa kwamitin COSMO | Siyasa | DW | 04.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Magoya bayan Mahaman Ousmane a Nijar sun kafa kwamitin COSMO

Magoya bayan tsohon shugaban jam'iyyar CDS Rahama kana zababben shugaban kasar Nijar na farko sun kafa wannan kwamiti ne domin goyon bayan takararsa a zabe mai zuwa.

Kafa wannan komiti na COSMO ya wakana ne bayan da shugabancin jam'iyyarsa ta asali ta CDS Rahama ya kubuce masa a sakamakon kayin da abokin hamayyarsa cikin rikicin neman shugabancin jam'iyyar Alhaji Abdou Labo ya yi masa a gaban kotu.

Bikin kaddamar da wannan kwamiti na goyan bayan Mahaman Usmane ya samu halartar Shugabannin 'yan adawa da dama wadanda a gurin bikin suka sha alwashin tsayawa takara ko ana ha maza ha mata a zaben shugaban kasar mai zuwa duk da tuhume-tuhumen da suke fuskanta gaban kotu.

Tuhume-tuhuman kuma da suke zargin gwamnatin Mahamadu Issoufou da kitsa su domin haramta masu kalubalantarsa a zaben mai zuwa. Zargin da bangaren shugaban kasar ke musantawa.

Sauti da bidiyo akan labarin