1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Macron da Merkel za su tattauna da Rasha

Mouhamadou Awal Balarabe
June 19, 2021

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron sun samu kusancin ra'ayi kan yadda za su yi hulda da Turkiyya da Rasha nan gaba duk da sabanin da ke tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/3vCmU
Deutschland Treffen Merkel und Macron in Berlin
Hoto: Michael Sohn/AP Photo/picture alliance

Jamus da Faransa sun cimma matsaya kan yadda za su yi hulda da kasashen Turkiyya da Rasha a nan gaba. Bayan wata liyafar cin abincin dare da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi da shugaban Faransa Emmanuel Macron a birnin Berlin, ta ce tana ganin cewa Kungiyar Tarayyar Turai na fuskantar manyan matsaloli game da kasashen biyu. Amma kuma dogara da juna da sassa biyu ke yi a fannoni da dama ya sa  dole su ci gaba da tattaunawa da kasashen biyu, shawarar da Shugaba Macron ya amince da ita. 

Sai dai jagororin biyu sun nuna damuwa game da yiwuwar yaduwar sabon nau'in Delta na cutar corona a gasar Kwallon Kafa ta kasashen Turai musamman a Birtaniya, inda anan ma ake gudanar da wasu daga cikin wasanni.