Mace mai wanki da guga a Najeriya | Himma dai Matasa | DW | 16.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Mace mai wanki da guga a Najeriya

Wata matashiya a jihar Bauchi da ke yin sana'ar wanki da guga ta bayyana cewa zuwa yanzu kasuwancinta ya bunkasa har ma ta kai ga daukar matasa maza da mata a karkashinta.

Symbolbild Slum Armut Ghetto Wäsche (Fotolia/bruder jakob)

Wata matashiya na yin sana'ar wanki da guga a Bauchin Najeriya

A cewar matashiyar mai suna Hajara wacce aka fi sani da suna Walida babu maraya sai rago, musamman idan aka yi la'akari da duniyar yau mai cike da kalubale ga duk wanda ya rungume hannayensa ya zama dan kallo, a cewarta babu shakka yana tare da takaicin rayuwa. Ta ce wannan ya sa ta ga hanya daya da za ta fitar da mutum cikin wannan hali shi ne ya kama sana'a, inda ta ce dalili ke nan da ya sanya ta fara sana'ar ta wanki da guga.

Haka zalika matashiyar ta bayyana cewa duk da tarin nasarorin da ta cimma cikin sana'ar, akwai kuma dumbin matsololi da suke damun ta. Za dai a iya cewa walida ta fita zakka, ganin cewa wasu daga cikin matasa ba su cika son neman na kansu ta hanyar kama sana'a ba, musamman ma mata.

Sauti da bidiyo akan labarin