Mace mai sana′ar gini | Himma dai Matasa | DW | 07.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Mace mai sana'ar gini

Zainab Muhammad Yoyo ta zama abin kwatance bayan da ta rungumi sana'ar gini da ake ganin sana'a ce ta maza zalla musanman ma a yankin Hausa na Arewacin Najeriya.

Zainab Muhammad Yoyo, matashiya ce wacce ta yi karatu har ta sami shaidar koyarwa ta NCE, duk da ta sami aikin koyarwa a jihar Kano, ta ce abin da take samu na albashi ba ya iya gamsar da ita wajen harkokin yau da gobe balle akai ga biyan kudin makarantar yaranta, dalilin da yasa ta shiga sana'ar aikin gini kenan.


Duk da cewa ta samu biyan bukata ba tare da kulawar miji ba amma tayi kira ga maza da su kula da hakkin da ke kansu na biya wa matansu bukatun yau da kullum. Daga karshe Zainab ta ja hankalin matasa musamman mata, dasu rungumi sana'ar hannu domin dogaro da kai.

Sauti da bidiyo akan labarin