1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace-macen Coronavirus a China ya kai 1500

Abdullahi Tanko Bala
February 14, 2020

Yawan mutanen da suka mutu a sanadiyar kwayar cutar Coronavirus a lardin Hubei na China ya karu zuwa mutum 1380 a cewar hukumar lafiya ta lardin

https://p.dw.com/p/3Xl9u
China Wuhan Jinyintan Hospital
Hoto: picture-alliance/AP/Chinatopix

Daga cikin karin mutane 116 da suka rasu 88 daga cikinsu suna lardin Wuhan ne inda aka fara samun bullar kwayar cutar a bara.
Hukumar lafiyar ta ce an sabbin kamun cutar har mutum 4,823 a Hubei wanda ya kai adadin wadanda ke dauke da kwayar cutar a lardin zuwa 55, 748


Karin adadin na zuwa ne bayan mutuwar mutane 242 da kuma sabbin kamu 14,000 kawo yanzu kwayar cutar ta Coronavirus ta yadu a kasashe 27 bayan China.


Ministan lafiya na Jamus Jens Spahn ya shaidawa tashar DW cewa ana cigaba da kokari na gano cutar da kuma daukar matakan dakile ita a tsakanin kasashen Turai. Ya jaddada bukatar hada hannu domin ganin cutar bata zama babbar annoba a duniya baki daya ba.