Luguden wuta a iyakar Iraki da Siriya | Labarai | DW | 28.06.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Luguden wuta a iyakar Iraki da Siriya

Wani luguden wutar da sojojin Amirka suka yi a kan sansanonin mayakan sa kai da ke samun goyon bayan Iran a iyakar kasashen Iraki da Siriya ya hallaka akalla mutun biyar.

Kakakin ma'aikatar tsaron Amirka ta Pentagon John Kirby, ya ce shugaba Joe Biden da kansa ne ya umarci kaddamar da harin, kana kuma tuni aka samu nasarar lalata wasu wuraren ajiyar makamai biyu a Siriya da kuma wani sansani guda a Iraki.

Ko baya ga wadanda suka halaka, wata kungiyar kare hakkin bani Adama da ke sa ido kan Siriya da ke birnin Landan, ta ce an jikkata wasu mutane da dama a samamen da ke zaman irinsa na biyu kan mayakan sa kan da ke samun goyon bayan Iran, tun bayan darewar shugaba Joe Biden a kan madafan iko.