Likitan kasar Kwango ya samu kyautar Kungiyar Tarayyar Turai | Labarai | DW | 26.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Likitan kasar Kwango ya samu kyautar Kungiyar Tarayyar Turai

Likitan ya samu wannan karramawa saboda irin gudunmawar da yake ba wa mata musamman wadanda suka fuskanci fyade a lokutan yaki.

Dakta Denis Mukwege, da ya zama likita dan kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango da ya samu lambar yabo ta majalisar Tarayyar Turai ya yi kira ga kasashen duniya da su bada duk gudunmawar da ta dace wajen kawo karshen cin zarafin mata ta hanyar fyade.

Dakta Denis mai shekaru 59 da ya yi suna a Jamhuriyar Demokradiyar Kwango da ma wasu sassan duniya, ya samu lambobi da yawa na girmamawa saboda irin gudunmawar da yake bayarwa a yaki da cin zarafin mata, lamarin da ya ba shi dama ta samun karramawa da wannan lamba da majalisar Tarayyar Turan da zai samu dubu hamsin na Euro. Ya ce zai amfani da kudin a ayyukan na sadaukarwa, kamar yadda Dakta Denis Mukwege ke cewa:

"Muna da wani shiri a asibitin Paziye wanda zai ba wa matan da muke kula da su jari da za su gudanar da sana'a bayan sun warke. Wannan shirin zai ba wa mata damar sarrafa albarkatun noma. Wannan zai ba su damar sayar da albarkatun nomansu a farashin da ya dace. Wannan kudi kuma zai ba su damar kula da karatun 'ya'yansu."