Libiya: Al-Sisi ya gargadi kasashen yamma | Labarai | DW | 17.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Libiya: Al-Sisi ya gargadi kasashen yamma

A wani mataki na neman kauce wa fadawa 'yar gidan jiya, shugaban kasar Masar ya yi hannunka mai sanda ga kasashen Yamma kan batun daukan matakin soja a Libiya.

Ägypten Präsident Abdel Fattah al-Sisi

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah Al-Sisi

Shugaban na Masar Abdel Fattah Al-Sissi dai ya yi hannunka mai sanda ne ga shugabannin kasashen Yamma dangane da daukan duk wani matakin soja na gaggawa a kasar Libiya, inda ya ce ya kyautu a ce shugabannin sun koyi darasi daga yakin da suka yi a kasashe irin su Somaliya da Afghanistan.

Cikin wata hira ce dai da wata jaridar kasar Italiya ta yi da shi, Shugaba Al-Sissi ya ce yana da mahimmanci duk wani matakin soja da kasar Italiya, ko faransa ko ma sauran kasashen duniya za su dauka, su dauke shi har idan gwamnatin kasar ta Libiya ce ta bukaci hakan, kuma ya kasance a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.

Daga bisani shugaban na Masar ya ce su Turawa suna yi wa kasar ta Libiya kallon tamkar matsalar ta itace ta 'yan kungiyar IS, alhali kuwa abun ba haka yake ba a cewar sa, domin akwai kungiyoyi da dama na mayaka da ke da iri-irin wannan akida ta 'yan IS.