Lavrov a Washington
May 10, 2017Talla
Ganawar ta shugaban na Amirka Donald Trump da Sergei Lavrov, zai mayar da hankali ne kan batun samar da tuddan mun tsira a yankunan kasar Syria da ke fama da yake-yake.
Ziyarar dai na zuwa ne sa'o'i bayan sanar da sallamar shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta FBI James Comey.
Bayanai na nunin cewa sallamar jami'in na da nasaba da bincike da ya jagoranta dangane da alakar yakin neman zaben Donald Trump da kuma Rasha.
Sai kuma yadda ya yi aiki a kan sakonnin e-mel din 'yar takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar Democrat da ta sha kayi, wato madam Hillary Clinton.