Lagarde: Dole a sasanta rikicin kasuwanci | Labarai | DW | 11.10.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lagarde: Dole a sasanta rikicin kasuwanci

Shugabar Asusun bada Lamuni na duniya, ta yi kira ga kasashen Amurka da China da su sasanta rikicinsu na kasuwanci, tare da aiki tare domin samar da mafita kan dokokin kasuwanci a maimakon tarwatsasu.

A jawabinta na kaddamar da taron hadin gwiwa na shekara-shekara tsakanin babban bankin duniya da hukumar ta IMF a tsibirin Bali da ke kasar Indonesiya, Christine Lagarde ta ce yin hakan ne kawai zai samar da mafita tare da ceto kananan kasashe da wannan rikicin ka iya shafa.

" Muna kira da a kawo karshen wannan rikici, ta hanyar zama teburin sulhu domin inganta tsarin kamar yadda yake, yadda kowa zai ci moriyarsa ta hanyoyi da dama ba tare da cutarwa ba, musamman a bangaren wadanda ke dogaro da wadannan manyan kasashe a harkar kasuwanci".

Ta kara da cewar takaddamar da ke tsakaninsu na da tasiri sosai ga makomar tattalin arzikin kasashen duniya.