1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin wasanni: Dortmund ta sallami kocinta

Lateefa Mustapha Ja'afar MNA
December 14, 2020

Bayan kwashe tsawon watanni 29 yana horar da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund, a karshe kungiyar ta sallami mai horas da 'yan wasan nata Lucien Favre.

https://p.dw.com/p/3mhyM
BVB | Lucien Favre
Hoto: Lars Baron/Getty Images

Za mu yaye kallabin shirin na wannan rana da wasan dambe, inda fitaccen dan wasan damben nan na Birtaniya ajin masu nauyi da ke da asali da Najeriya wato Anthony Joshua ya ci gaba da rike kambunsa na zakaran wasan damben bayan da ya samu nasara a kan abokin karawarsa Kubrat Pulev a karshen mako. Joshua ya yi kaka-gida, inda a karshe dai bayan sun fafata turmi takwas babu kisa ya samu nasarar kashe Pulev a turmi na tara. A hirar da ya yi da manema labarai, Joshua ya ce karawar da za su yi da wanda ke rike da kambun duniya na ajin masu nauyin wato Tyson Fury a shekara mai zuwa ta 2021, za ta fito da kwarewarsa fili. Koda yake Fury wanda aka kasa kashewa a wasannin dambe har 31, ya bayyana cikin wani faifen bidiyo a shafukan sada zumunta cewa zai kashe Joshua tun a turmi na uku, sai dai Joshua ya ce ko ba komai dai zai fafata da fitaccen dan damben duniya Fury.

Anthony Joshua bayan nasarar doke Kubra Pulev a damben ajin masu nauyi a Wembley, London
Anthony Joshua bayan nasarar doke Kubra Pulev a damben ajin masu nauyi a Wembley, LondonHoto: Andrew Couldridge/Pool/picture alliance

A gasar Bundesligar kasar Jamus, kuwa a karshen mako wasa bai yi wa kungiyar Borussia Dortmund dadi ba, domin kuwa kungiyar Stuttgart ta bi ta har gida ta kuma lallasa ta da ci biyar da daya. Sai dai kwana guda bayan wannan abin kunya, kungiyar ta sanar da korar mai horas da 'yan wasanta Lucien Favre, wanda ya kwashe tsawon watanni 29 yana horas da 'yan wasan na Dortmund. Sai dai rashin nasarar da kungiyar ke yi musamman a gida ya tilasta daukar wannan mataki a kansa. Mai shekaru 63 a duniya, Favre ya fara horas da 'yan kungiyar ta Borussia Dortmund a shekara ta 2018, ya kuma taba zama mai horas da 'yan wasa a kungiyoyin kwallon kafa na Hertha Berlin da Borussia Moenchengladbach.

A sauran wasanni da aka fafata a karshen mako, an tashi wasa tsakanin Wolfsburg da Frankfurt biyu da daya, Freiburg ta lallasa Armenia Bielefeld da ci biyu da nema, Mainz kuwa ta sha kashi a hannun Kolon da ci daya mai ban haushi.

Bayer 04 Leverkusen ta haye saman teburin Bundesliga baya ta lallasa Hoffenheim da ci 4 da 1
Bayer 04 Leverkusen ta haye saman teburin Bundesliga baya ta lallasa Hoffenheim da ci 4 da 1Hoto: Thilo Schmuelgen/AFP/Getty Images

An kuma tashi wasa kunne doki daya da daya a fafatawar da aka yi tsakanin Borossia Moenschengladbach da Herther Berlin, yayin da a gumurzun da aka yi tsakanin RB Leipzig da Werder Bremen aka tashi wasa Leipzig na da ci biyu Bremen na nema.

Ita kuwa Bayern Munich wasan bai mata dadi ba, domin kuwa a karawarsu da Union Berlin sun tashi ne kunne doki daya da daya. A ranar Lahadi kuwa, Augsburg da Shalke sun tashi wasa canjaras biyu da biyu yayin da Leverkusen ta kasa ta tsare a gida, inda ta yi wa Hoffenheim fata-fata da ci hudu da daya. Wannan nasara dai ta bai wa Leverkusen din damar darewa kan teburin na Bundesliga da maki 25 yayin da Bayern da Leipzig ke biye mata a matsayi na biyu da na uku da maki 24 kowaccensu, sai Wolfsburg a matsayi na hudu da 21 yayin da Dormund ke a matsayi na biyar da maki 19.