Labarin wasanni: Aljeriya da Senegal sun kai wasan karshe na AFCON | Zamantakewa | DW | 15.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Labarin wasanni: Aljeriya da Senegal sun kai wasan karshe na AFCON

Aljeriya da Senegal sun yi nasarar kaiwa wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka a kasar Masar bayan da suka kori Tunusiya da Najeriya a wasannin kusa da na karshe.

Saurari sauti 09:56

Aski ya zo gaban goshi a kokarin da kasashen Afirka ke yi na neman lashe kofin kwallon kafa na wannan nahiya, inda bayan tankade da rairaya Senegal da kuma Aljeriya suka kai bantensu zuwa zagayen karshe. Ita dai kungiyar kwallon kafa ta Senegal ta yi nasarar yin waje rod da Tunisiya bayan da ta doke ta da ci daya mai ban haushi a yayinda Aljeriya ta doke Najeriya. A ranar Jumma'a ne za a buga wasan na karshe tsakanin Alejriya da ke neman lashe kofin a karo na biyu da kuma Senegal da ke neman lashe kofin a karon farko cikin tarihinta.