Labarin wasanni: 29.04.2019 | Zamantakewa | DW | 29.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Labarin wasanni: 29.04.2019

Kasar Kamaru ta lashe kofin kwallon kafa na Afirka na 'yan kasa da shekaru 17 da haihuwa.

A cikin na wannan lokaci za ku ji cewa duk da kashin da ta sha a gida a gaban kishiyarta ta Schalke 04 kungiyar Dortmund na da sauran lakonta a game da yiwuwar lashe gasar Bundesligar ta bana. A kasar Spain kungiyar barcelona ta lashe gasar La Liga ta shekarar bana. A nahiyar Afirka kuwa kasar Kamaru ta lashe kofin kwallon kafa na Afirka na 'yan kasa da shekaru 17.

A wasan hamayyar kishiyoyi mafi tasiri a gasar Bundesligar kasar Jamus tsakanin Kungiyar Dortmund da babbar kishiyarta ta Schalke 04 a filin wasa na Signa Iduna Park, inda a wannan karon batta da ke zama na 94 tsakanin wadannan kungiyoyi kishiyoyin juna, Dortmund da ke a matsayin ta biyu a saman tebirin Bundesliga ta kwashi kashinta a hannu da ci hudu da biyu a gida a gaban kungiyar Schalke 04 da ke a matsayin ta 15 a tebirin Bundesliga. Sai dai kuma duk da haka har ya zuwa yanzu Dortmund da ke a matsayin ta biyu da maki 69 na da sauran lakonta a sukuwar neman lashe gasar ta Bundesliga ta bana, kasancewa Yaya Babba Bayern Münich ta kasa kai bantanta a ranar Lahadi a gaban kungiyar Nüremberg inda suka tashi kunnan doki da ci daya da daya wanda ke nufin cewa tazarar maki biyu ce kawai ke da akwai tsakaninta da Dortmund a lokacin da ya rage wasanni uku a kammala gasar Bundesligar ta bana inda komi na iya faruwa a nan gaba.

Fußball Bundesliga 31. Spieltag l BVB Dortmund vs FC Schalke 04 l Tor 1:2 Jubel (Getty Images/Bongarts/S. Franklin)

Salif Sane na Schalke 04 bayan ya ci kwallo na biyu a karawarsu da Dortmund

A kasar Spaniya kuwa gayya ta kare aiki a wannan mako a wasannin La Liga, inda Kungiyar Barcelona a karkashin jagorancin dan Aljantina Leonel Messi ta lashe gasar ta bana da maki 83,  bayan da a ranar Asabar ta doke kungiyar Levante da ci daya mai ban haushi. Leonel Messi ne ya ci wa kungiyarsa daya dayar kwallon a minti na 62.

Wannan shi ne karo na 26 da Barcelona ke lashe gasar ta La liga wacce ta dauka so takwas a cikin shekaru 11 kacal. Kuma wannan shi ne karo na 10 da dan Aljantinar ya lashe La Ligar.

 A daidai lokacin da Messi ya kafa bajintar lashe gasar La Liga karo na 10 a Spaniya shi ma dai daga nashi bangare babban abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo da ke bugawa kungiyar Juventus a gasar Seria ta kasar Italiya ya sake kafa wani tarihin na dabam, inda a karawar da kungiyarsa ta yi da Inter Milan a wasannin mako na 34 ya yi nasarar zura kwallonsa ta 600 a wasannin Lig-lig hudu na Turai wato biyar a kungiyar Sporting Lisbonne, kwallaye 118 a Man United, 450 a Real Madrid kana 27 a Kungiyar Juventus. Kwallaye uku ne suka rage wa abokin hamayyarasa Leonel Messi ya shiga shi ma sahun 'yan kwallon da suka ci kwallaye 600 a wasannin Lig-lig na Turai.

Spanien Fußball FC Barcelona - UD Levante Lionel Messi (picture-alliance/AP Photo/M. Fernandez)

Lionel Messi na murnar cin a karawa tsakanin kungiyarsa ta Barcelona da Levante

Sai dai a wannan mako wani abin da ya fi ba da mamaki a hamayyar da ke da akwai tsakanin 'yan wasan biyu shi ne irin yadda a ranar Asabar da ta gabata duk da kasancewa wannan na Spaniya wannan kuma na Italiya suka yi nasarar zura kwallo a rana daya a lokaci daya da kuma kafa daya wato ta hagu a minti na 62. Wani lamarin da ya kara tabbatar da karfi da kuma saddabarun da ke tattare da hamayyar wadannan 'yan wasa biyu da taurarunsu suka share shekaru sama da 10 suna ci gaba da haskawa a duniyar kwallon kafa.

Har yanzu dai muna kan batun kwallon kafan amma a wannan karo a nahiyar Afirka inda a ranar Lahadi kasar Kamaru ta lashe kofin kwallon kafa na Afirka na 'yan kasa da shekaru 17 bayan da ta doke kasar Guinea da ci 5-4 a bugon daka kai sai mai tsaron gida a fafatawar da suka yi a filin wasa na birnin Dar-es Salam na kasar Tanzaniya.

Sauti da bidiyo akan labarin