Labaran Maku ya sha kaye a zaben PDP | Labarai | DW | 09.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Labaran Maku ya sha kaye a zaben PDP

Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta zabi wadanda za su tsaya mata takarar kujerar gwamna a zeben 2015 a jihohin Plateau da Nasarawa, inda Maku ya kasa Kai labari.

Jamiyyar PDP mai mulki a Najeriya ta sanar da sakamakon zaben fin da gwani na yan takarar kujerar gwamna a jihohin Plateau da Nasarawa.

A jihar Filato dai jam'iyyar ta zabi Senata (JNS)GNS Pwajok ne da kuri'u 435, inda yayi nasara kan wasu yan takara 14, cikinsu har da mataimakin gwamnan jihar Mr. Ignatius Longjan wanda ya sami kuri'u 163.

Wakilin mu Abdullahi Maidawa Kurgwi, yace cikin fushi ne dai mataimakin gwamnan jihar ta Filato ya fice daga harabar zaben, sakamakon wani abinda ya bayyana da magudin da aka shirya shi a zaben .

A jihar Nsarawa ma dai a cikin dare ne jam'iyyar ta PDP ta fitar da Yusuf Agabi a matsayin dan tajkarar gwamna da kuri'u 214, inda ya doke shauran yan takara irinsu tsohon ministan watsa labarai Labaran Maku, wanda ya sami kuri'u 160, a zaben na jiya.

Yanzu dai Agabi zai fafata ne da gwamnan jihar Nasarawa Tanko Almakura a babban zaben kasa mai zuwa .