1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kyiv za ta tsaurara tsaro saboda barazanar Rasha

March 28, 2024

Ukraine za ta kara tsaurara matakan tsaro a Kyiv sakamakon hare-haren Rasha mussaman a kan cibiyoyin makamashinta.

https://p.dw.com/p/4eDwG
Rasha na zafafa kai hare-hare kan Ukraine
Rasha na zafafa kai hare-hare kan UkraineHoto: Solomiansky cats

Hukumomi a Ukraine na cewa, za a tsaurara matakai a babban birnin kasar Kyiv sakamakon zafafa kai hare-haren makamai masu linzami da Rasha ke yi a baya-bayan nan. Rasha ta kai jerin hare-hare ta sama kan cibiyoyin makamashin Ukraine a makon da ya gabata a wani mataki na ramuwar gayya kan hare-haren da Kyiv ta kaddamar a yankunanta.

Karin bayani: Rasha ta kai sabbin hare hare wajen Kyiv

Guda daga cikin shugabannin tsaro na Kyiv, Serhiy Popko ya ce kwamittin tsaro na duba yadda ake gudanar da taruka da ma inganta tsaro a wajen taruwar jama'a. Ya kara da cewa, za a dauki wannan matakin ne sakamakon yadda makaman da dakarun Rasha ke harbawa ke yin barna cikin kiftawar ido. Sai dai kuma Popko ya bukaci mazauna Kyiv da su kwantar da hankulansu yayin da gwamnati ke iyakar kokarinta na tsare rayukan jama'a.

Ukraine dai na yawan mika bukatar samun karin tallafin makamai daga kawayenta na yammacin Turai domin ta kare kanta daga hare-haren makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuka daga Rasha.