1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kura ta lafa a rikicin Isra'ila da Falasdinu

August 8, 2022

An tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da mayakan Islamic Jihad na yankin Falasdinu, sabon rikicin da ya yi sanadin salwantar falasdinawa da ma firgita dubban Isra'ilawa.

https://p.dw.com/p/4FF1M
Palästinenser suchen in den Trümmern eines Wohnhauses
Hoto: Ismael Mohamad/UPI/IMAGO

Yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da mayakan Islamic Jihad na falasdinu ta fara aiki, a kokarin kawo karshen sabon tashin hankalin da ya taso tsakanin bangarorin biyu da ya salwantar da gomman falasinawa tare da taba rayuwar wasu dubban daruruwan Isra'ilawa.

Wannan ne dai rikici mafi muni da aka gani tsakanin Isra'ila da 'yan tada kayar baya na zirin Gaza, tun baya wani fada na kwanaki 11 da aka gwabza a bara.

Yarjejeniyar da Masar ta shiga tsakani dai ta fara aiki ne da misalin karfe 11:30 na daren jiya.

Sai dai bayanai na cewa Isra'ila ta harba rokoki a kan wasu yankuna na Gaza mintuna kalilan da yarjejeniyar ta fara aiki.

Isra'ilar na cewa tana neman mayakan na jihadi ne, mahukunta a Gaza sun ce fararen hula ne take kashewa.

Tuni ma dai shugaban Amirka Joe Biden, ya yi marhabin da tsagaita bude wutar, rikicin dai ya yi sanadiyyar mutuwar akalla falasdinawa 44 da suka hada da kananan yara 15 cikin kwanaki uku.