1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 60 da kafa kungiyar OPEC

September 14, 2020

A yayin da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur a duniya OPEC ke cika shekaru 60 da kafuwa, masu ruwa da tsaki a harkar man Najeriya, sun ce ta yi rawar gani wajen habaka tattalin arziki da ma zamantakewa a kasar.

https://p.dw.com/p/3iT4K
Symbolbild OPEC, Organisation Erdöl exportierender Länder
Shekaru 60 da kafa kungiyar kasashe masu arzikin man fetur wato OPECHoto: picture-alliance/dpa/B. Gindl

An dai kafa kungiyar OPEC din ta kasashe masu arzikin man fetur a duniya ne da nufin taka birki dangane da rawar da kamfanonin Amirka ke takawa a cikin masana'antar man mai tasiri. Sai dai kuma bayan shekaru 60 tana taka rawa a kokari na daidaiton lamura a cikin masana'antar, ra'ayi na bambanta a cikin Tarayyar Najeriya, dangane da rawa da ma tasiri na kungiyar a cikin masana'antar mai ta kasar.

Karin Bayani: Najeriya: Martani kan farashin man fetur

OPEC din dai ta taka rawar daidaita farashi da ma yawan man da kasashe na kungiyar ke iya samu da nufin tsari da tabbatar da cin moriyar hajar man tsakanin kasashen kungiyar. Kaso 90 cikin dari na arzikin Najeriyar dai na zuwa ne daga hajar man da kasar ta share shekara da shekaru tana samarwa. Kuma OPEC na zaman ta kan gaba wajen tabbatar da kyautata farashin man da ya taka rawa wajen ginin kasar tun bayan 'yancin kai ya zuwa ga annobar COVID-19
Lawal Habib dai na zaman  masanin tattalin arzikin da ya ce OPEC ta zamo uwar da ta dauki lokaci tana shayar da kasar a kan hanyar dora ta zuwa girman da take da bukata. Kokari na samar da kariya ga batu na fasahar mai ko kuma mai da ta zuwa 'yar mowa  dai,  kariyar ta OPEC ce ake yi wa kallon ummul aba'isin mantawar kasar da mayar da hankali ya zuwa sassa dabam-dabam na tattalin arzikin da take da bukata baya.

Erdölindustrie in Nigeria
Cire tallafin mai a Najeriya, ya taimaka wajen shigar talakawa halin kunciHoto: picture-alliance/dpa/EPA/STR

Kafin rikicin na faduwar farashin man fetur gami da lalacewar ababen more rayuwa dai, man na zaman jagora na walwala da kuma nuna halin ko in kular a cikin harkokin noma da ma'adinai da ma bukatar gina masana'antu na sarrafa a tsakanin al'umma. Kuma a fadar Dakta Garba  Ibrahim Malumfashi da ke zaman tsohon mashawarci a kungiyar ta OPEC, hakan ya janyowa kasar koma baya na lokaci mai tsawo, idan aka kwatanta da kawayen samun 'yancinta na baya.

Karin Bayani: Gwamnatin Najeriya ta cire tallafin mai

Rawar hajar man wajen baro Najeriyar a cikin fatara dai, daga dukkan alamu na da ruwa da tsaki da sauyi na rawa da kila ma sababbin manufofin 'yan mulki na kasar.