1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faduwar farashin mai za ta jefa Najeriya cikin matsala

Muhammad Bello MAB
December 27, 2018

Kungiyar kasashe masu arzikin danyen mai ta OPEC ta sanar da faduwar farashin mai a kasuwannin Duniya, Sai dai da alamu matakin zai yi babbar illa ga kasafin kudin Najeriya na 2019 kasancewa kasar na dogaro a kan fetur.

https://p.dw.com/p/3AhFg
Nigeria Port Harcourt Arbeiter auf Plattform Ölförderung
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

OPEC ta ce man fetur ya fadi zuwa dala hamsin a kan ganga daya ,lamarin da ya gaza da dala goma ga farashin dala 60 da aka daidaita kasafin kudin shekarar 2019 na Najeriya. Hakan na nufin sabon kalubale ga aiwatuwar da kasafin na kudi tun ma ba a je ko'ina ba. Ita dai kungiyar ta OPEC ta nunar cewar tana iya kokari domin cimma daidaiton farashin na mai don tabbatar da kasashen masu mai ba su fada cikin rikici ba.

Tun daga lokacin da Donald Trump shugaban Amirka ya hau mulki, ya samu hadin kan kasar Saudi Arabiyya tare da shiga rigima da kasar Iran, lamarin da ya sa harkar OPEC ta rikice. Yanzu ma haka kasar Qatar na kokarin ficewa daga tsarin OPEC, kuma yawancin mambobinta sun daina bin umarnin kididdigar yawan man fetur da ake basu damar hakowa. Wannan al'amari na da nasaba da halayyar wasu kasashe da suke da mai amma ba sa cikin kungiyar.    

Nigeria Lagos Benzinpreis
Fetur na karanci a gidajen mai duk da arzikin mai da Najeriya ke da shiHoto: Getty Images/AFP/P.U. Ekpei

Evelyn Brightda ke zaman ma'aikaciyar gidan Rediyo na Jahar Rivers, da kuma ke sharhi kan al'amura daban-daban cewa ta yi.

"hakan na nufin za'a kara shiga matsatsi ke nan,lamarin ba zai yi kyau ba, dole ne mu tashi tsaye, mahukunta su lalubo mafita domin matasanmu da yanzu ke haifar da damu. Damuwar tada kayar baya za ta iya karuwa muddin rayuwa ta kara tsananta. "

Najeriya dai ta takwas ce a jerin kasashe masu arzikin man fetur a Duniya. Tana da karfin iya hakar gangar ta danyen mai miliyan biyu a kullum. Cinikin danyen mai da kasar ta yi na tsawon shekaru na biliyoyin daloli,ya kai ga 'yan kasar su fahimci wani abu na game da samar da ababen more rayuwa.