Kungiyar EU ta rubanya tallafi a aikin ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 24.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar EU ta rubanya tallafi a aikin 'yan gudun hijira

Gawarwaki 24 ne kawai aka gano cikin kimanin bakin haure 800 da suka rasu a tekun , a bala'in da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana da cewa shi ne mafi muni.

EU Sondergipfel Renzi & Merkel & Hollande & Cameron

Manyan shugabanni daga cikin kungiyar kasashen Turai

Kasashen Turai sun amince a jiya Alhamis a zaman taronsu na gaggawa a birnin Brussels na Belgium cewa, zasu rubanya kudade har sau uku na abinda zasu kashe a ayyukan ceto da sintirin dakarunsu cikin teku, dan dakile masu fasakaurin al'umma, idan ta kama har da amfani da karfin soji. Matakin da ke zuwa bayan mutuwar daruruwan bakin haure a cikin tekun Bahar Rum a karshen makon da ya gabata.

Gawarwaki 24 ne kawai aka gano cikin kimanin bakin haure 800 da suka rasu a tekun, a bala'in da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana da cewa shi ne mafi muni cikin bala'oin da suka faru cikin tekun na Bahar Rum a tarihi na baya-bayannan.

A cewar Firaminisatan Italiya Matteo Renzi wanann mataki da kasashen na Turai suka dauka a jiya Alhamis na zama mai mahimanci cikin irin kokarin da kasashe za su yi na ganin an dakile halakar da baki masu burin zuwa Turai.