Kundin zabe na musamman a Nijar | Siyasa | DW | 04.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kundin zabe na musamman a Nijar

Wannan shi ne karon farko da kasar zata yi amfani da wannan kundin zabe na zamani da zai kunshi bayanai na masu kada kuri'a tare da bai wa yan kasar da ke waje dama.

A jamhuriyar Nijar hukumomin kasar sun rantsar da mambobin kwamitin rubuta sunayen masu zabe a wani kundin rijistar masu zabe na zamani da kasar ta Nijar ke son amfani da shi a yayin zabubukan da ke tafe wanda ake hasashen farawa a wannan shekarar.

Wahlen im Niger

A tsakiyar watan satumban wannan shekarar dai ne kwamitin ya kayyade damka sabon girgam din mai kumshe da sunayen 'yan kasar ta Nijar da suka cancanci jefa kuri’a a yayin zabubukan dake tafe, inda kawo yanzu kwamitin mai kumshe da mambobi da dama da suka hada da 'yan siyasa al’kalai da kungiyoyin fararen hulla suka fara aiki gadan gadan domin samar da wannan sabon kundin a cikin lokaci.

wannan shine karon farko kenan da kasar ta Nijar za ta yi amfani da wani kundi na zamani domin gudanar da zabe, zaben da a cikinsa 'yan kasar da ke ketare zasu samu damar jefa kuri’arsu a duk inda suka kasance,to amma sai dai tuni jam’iyyun adawar kasar suka fara korafin rashin wadataccen lokaci ga kwamitin muddin ana son samarda wani tsabtatacen kundin.
Mourtala Alhaji Mamouda kakakin jam’iyyun adawa ne:

Wahlen im Niger

"A yau din ma inda matsalar take kwamitin sai ya kirga 'yan Nijar kuma ba’abasu kayan aiki ba, kuma ma basu fara aikin ba,abu na biyu can a kasashen waje sai an tantance suwaye ya kamata su yi zabe, kaje bakada takardu cikakku ace zakayi zabe kenan bata yiwa kayi zabe a wata kasa ba ka da takardun Nijar,kenan kaga a cikin watnni hudu ko bakwai ba ya yuwa a ce anyi wannan aikin".

Babban kalubalen da ke gaban kwamitin shi ne na tantance 'yan kasar ta Nijar na ciki da na wajen kasar a matakin farko, kafin rubuta sunayensu a sabon kundin wanda wasu akasarin 'yan kasar ta nijer din musamman mazauna karkara nada rauni wajan samun cikakkun takardun da hukumar zata yi amfani da su domin rubuta su a cikin kundin,to amma sai dai a cewar Malam Yahaya Garba mamba a kwamitin, lokacin da suka dibarwa kansu zaya wadatas "Nan da wata bakwai ko takwas insh’Allahu zamu ida wannan aikin domin kafin mu fara saida munka ce aje a duba cikin kasashen da ke kusa da mu yaya ne sunkayi nasu sai munka ga wadansu sunyi nasu a cikin wata tara wasu a cikin shekaru biyu wasu a cikin shekaru uku idan kunka tsara shi ya dauki shekaru sai yayi shekaru idan kuma kunka tsara don ya kammala a cikin lokaci kadan shikenan"

Sauti da bidiyo akan labarin