1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Kotun Illinois ta cire sunan Donald Trump daga takara

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 29, 2024

Makamancin wannan mataki ne kotun Colarado ta dauka, ko da yake batun yanzu yana gaban kotun kolin Amurka don jiran hukuncinta

https://p.dw.com/p/4d0Oe
Hoto: Andrew Harnik/AP Photo/picture alliance

Kotun jihar Illinois ta ba da umarnin cire sunan tsohon shugaban Amurka Donald Trump daga cikin zaben fitar da gwani na 'yan takarar shugaban kasa na Republican a jihar, sakamakon rawar da ya taka wajen ingiza magoya bayansa har suka farwa ginin majalisar dokokin kasar lokacin da yake kan karagar mulki.

Karin bayani:Donald Trump ya kayar da Nikki Haley a mahaifarta ta South Carolina

Tuni dai Mr Trump ya yi tir da hukuncin kotun, yana mai cewar siyasa ce kawai kuma babu adalci sam a ciki.

Karin bayani:Tsohon shugaban Amirka Donald Trump zai gurfana a gaban kotu a Maris

Makamancin wannan mataki ne kotun Colarado ta dauka, ko da yake batun yanzu yana gaban kotun kolin Amurka don jiran hukuncinta.

Colarado da kuma wasu jihohi sama 12 ne dai za su gudanar da zaben fitar da gwanin 'yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican a ranar 5 ga watan Maris mai kamawa.