1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Trump ya kayar da Nikki Haley a mahaifarta ta South Carolina

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 25, 2024

Hakan na nuni da cewa Mr Trump ya lashe dukkan zabukan fidda gwanin da aka yi a Iowa da New Hampshire da Nevada da kuma tsibiran U.S. Virgin Islands

https://p.dw.com/p/4cqhE
Hoto: Mike Stewart/AP Photo/picture alliance

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar Republican a jihar South Carolina cikin ruwan sanyi, inda ya doke tsohuwar jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley a garinta na haihuwa.

Karin bayani:Zaben fidda gwani na jam'iyyar Republican

Hakan na nuni da cewa Mr Trump ya lashe dukkan zabukan fidda gwanin da aka yi a Iowa da New Hampshire da Nevada da kuma

tsibiran U.S. Virgin Islands.

karin bayani:Trump ya zama dan takarar shugaban kasa a lowa

Wannan na nufin Mr Trump ya kama hanyar lashe kujerar takarar shugabancin kasar a jam'iyyar Republican, a daidai lokacin da ya ke fuskantar kalubalen shari'a kan laifukan da ake zargisa da aikatawa lokacin mulkinsa, wanda ka iya yi ma sa dabaibayin samun damar shiga babban zaben kasar da za a gudanar a cikin watan Nuwamban bana.