1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChadi

Kotu ta tsefe 'yan takara a zaben shugabancin Chadi

Mouhamadou Awal Balarabe Abdoulaye Mamane/Abdul-raheem Hassan
March 26, 2024

A kasar Chadi, ‘yan takarar shugabancin kasa goma ne ke cikin jerin sunayen da kotun kolin ta tantance, yayin da yi watsi da takara wasu goma daga cikin ashirin.

https://p.dw.com/p/4e8pE
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Chadi Mahamat Idriss Deby
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Chadi Mahamat Idriss DebyHoto: Gonzalo Fuentes/REUTERS

Kusan dalalai iri daya ne alkalai tara na kotun kare kundin tsarin mulkin kasar Chadisuka bayar, wajen yin watsi da takara goma a zaben shugaban kasa da zai gudana a ranar shida ga watan Mayun 2024.

Dukkaninsu na da alaka da takaddun haihuwa na 'yan tataka wadanda ba su dace da tanadin doka ba, kamar rashin daidaito game da wurin da aka haifi dan takara da kuma asalin kasar dan takara, sai dai lauya kuma dan rajin kare hakkin dan Adam Jean-Bosco Manga ya ce wadannan hujjoji ba su da tushe da makama.

Karin Bayani: Chadi: Succes Masra zai yi takara

"Dalilan suna da ban dariya idan a ka yi la'akari da wuraren haihuwar wadannan 'yan takara, 'yan kasar Chadi ne da ba a haife su a dakin haihuwa na asibiti ba, ko kuma ba a haife su a cibiyoyin da ke da wata karamar hukuma ko ofishin magajin gari da za ta iya yi musu takardar haihuwa da dai sauransu ba, ya kamata a yi la'akari da wadannan al'amura wajen yanke hukunci kan takardun haihuwar ‘yan kasar Chadi, domin idan haka ne da yawa za su kasance ba 'yan kasar Chadi ba ne."

Babban birnin N'Djamena na kasar Chadi
Babban birnin N'Djamena na kasar ChadiHoto: Denis Sassou Gueipeur/AFP

Mafi akasarin 'yan takarar da aka katse musu hanzari, shugabannin siyasa ne da suka fito daga arewacin Chadi, wasu sun fito ne daga lardi daya da shugaban gwamnatin mulkin soja Janar Mahamat Idriss Deby kamar Dokta Nassour Koursami. Wannan ne ya sa wasu masu lura da al'amuran siyasa ciki har da Nara Hantoloum, dan jarida na gidan rediyon Liberté ke ganin cewar, wannan wata dabara ce ta jagoran mulkin soja na zama dan takara tala tilo da ya fito daga Arewa a zaben shida ga watan Mayun 2024.

Karin Bayani : Mahamat Idriss Deby zai tsaya takarar shugabancin Chadi

"A cikin wadanda aka ki amincewa, takwas sun kasance ‘yan takara mabiya addinin Musulunci. Wannan ya karfafa zargin da ake cewar gwamnatin kasar Chadi ba ta son dan takara daga Arewa da zai kalubalanci Mahamat Deby a zabe."

Kiki-kakar kin amincewa da takarar shugabancin Chadi na zuwa ne kasa da wata guda bayan mutuwar babban dan hamayya Yaya Dillo Djérou, wanda sojoji suka kashe a ranar 28 ga watan Fabrairu a wani hari da suka kai hedkwatar jam'iyyarsa PSF.  

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch, ta yi kira da a kafa kwamitin bincike mai zaman kansa bisa taimakon kasashen waje, saboda mutuwar ta ya haifar da ayoyin tambayoyi game da dalilai na siyasa a yayin da zabe ke dada karatowa.

Yaya Dillo fitaccen dan adawar da aka kashe a kasar Chadi
Yaya Dillo fitaccen dan adawar da aka kashe a kasar Chadi Hoto: Issouf Sanogo/AFP

Karin Bayani: Chadi: Shirin zaben raba gardama kan kudin tsarin mulki

Duk da cewa an samu 'yan takara da dama a zaben shugaban kasar Chadi da zai gudana na ranar shida ga watan Mayu, amma manazarta da dama sun yi imanin cewa shugaban gwamnatin mulkin soja ne zai iya lashe zaben, saboda samun goyon bayan jam'iyyun siyasa sama da 200, kuma ya kakkange dukkan hukumomin da ke da alhakin shirya zaben kasar Chadi.