Chadi: An haramtawa 'yan adawa tsayawa takara
March 24, 2024Hukumomi a kasar Chadi sun haramtawa 'yan takara 10 daga neman kujerar shugaban kasa a zaben da za a gudanar a watan Mayaun wannan shekarar. Daga ciki wadanda aka dakatar har da mutum biyu daga cikin masu adawa da majalisar mulkin sojin kasar, yayin da sauran 'yan takara 10 da kotun tsarin mulkin kasar ta amince da takararsu har da shugaban gwamnatin mulkin soji Mahamat Idriss Deby Itno da kuma Firanminista Succes Masra.
Karin bayani:Mahamat Deby zai yi takarar shugabancin Chadi a 2024
Wannan dai shi ne karon farko a tarihin kasar Chadi da shugaban kasa da kuma Firanminista za su tsaya takarar neman dare wa kan madafun ikon kasar a lokaci guda. Sai dai 'yan adawa na cewa, Masra ya tsaya takara ne kawai domin ya halasta da zaben. Ana dai ganin Mahamat Deby ya samu nasara a zaben sakamakon manyan abokan hammayarsa sun mutu ko kuma su na gudun hijira. Ana sa ran a gudanar da zagayen farko na zaben a ranar 6 ga watan Mayu da kuma zagaye na biyu a ranar 22 ga watan Yunin wannan shekarar.