SiyasaJamus
Mahamat Idriss Deby zai tsaya takarar shugabancin Chadi
March 2, 2024Talla
Janar Mahamat wanda ya dare madafun iko bayan mutuwar mahaifinsa a shekarar 2021, ya yi alkawarin mayar da kasar kan mulkin dimukradiyya a watanni 18 kafin daga baya ya dage ranar zaben.
Dage ranar gudanar da zabe a Chadi ya janyo mumunar zanga-zanga da ta hallaka mutane sama da 50.
Sanarwar na zuwa ne kwanaki bayan kisan madugun adawa Yaya Dillo a wata arangama da jami'an tsaro a birnin Ndajamena.
Amma Kungiyar 'yan tawayen Chadi ta Front for Change and Concord da jam'iyyar adawa ta CNRD sun bayyana mutuwar Dillo a matsayin kisa don kawar da abokan hamayya.