Kotu ta soke zaben gwamnan jihar Rivers | Labarai | DW | 24.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta soke zaben gwamnan jihar Rivers

Kotun sauraron kararrakin zabe ta gwamnan jihar Rivers da ke kudu maso kudancin tarayyar Najeriya ta soke zaben da aka yi wa gwamna Nyesom Wike na jam'iyyar PDP.

A yau Asabar ne dai kotun ta yanke wannan hukunci a Abuja bayan da aka shafe makonni ana shari'a sakamakon karar da dan takara na jam'iyyar APC Dakuku Peterside ya shigar inda ya ke kalubalantar sakamakon zaben.

Kotun dai ta ce ta gamsu da shaidun da masu gabatar da kara suka shigar mata sannan kuma shaidun da wadanda ake kara suka bada ba abin dogaro ba ne, shi ne ma ya sanya ta ga dacewar soke zaben tare da bada umarnin gudanar da sabon zabe.

Tuni dai lauyoyin gwamnan na jihar ta Rivers suka ce za su daukaka kara saboda rashin gamsuwar da suka ce sun yi da hukuncin da kotun ta yanke.