Kotu ta saki ′yan adawa a Nijar | Labarai | DW | 23.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta saki 'yan adawa a Nijar

Bayan da aka zarge su da tada zaune tsaye, jami'an tsaro a Nijar sun kame daruruwan mutane yayin zanga-zangar adawa da jaridar Charlie Hebdo, da kuma ta 'yan adawar kasar masu adawa da wasu manufofin gwamnati.

A jamhurimruyar Nijar wata kotu ta bayar da belin wasu manyan 'yan adawar kasar da ke hannun jami'an 'yan sanda, biyo bayan zanga-zangar da aka yi da ta girgiza kasar. Sama da 'yan siyasa 60 ne akasarinsu mambobin jam'iyyun adawa, gwamnatin ta zarga da yin makarkashiya domin tayar da zaune tsaye. Cikinsu harda kakakin kawancen jam'iyyun adawar Husaini Tsalhatu da Umaru Dogari da Sumana sanda, tsohon ministan lafiyan kasar ta Nijar.

Mutane sama da 400 ne jami'an yan sanda suka chabke a makon jiya, sakamakon fitowar da dubban al'ummar kasar suka yi, domin zanga-zanga kan zanen batancin da jaridar charlie hebdo ta kasar Faransa ta yi ga fiyayyen halitta, inda a yammacin Jamma'ar nan,kotu ta saki akasarinsu a birnin Yamai.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Usman Shehu Usman