Kotu a Nijar ta Hukunta Samira Sabou
July 14, 2020Talla
A cikin watan Yuni da ya gabata ne aka kama Samira Sabou bayan da, dan shugaban kasar Nijar ya shigar da kara a gaban kotu a kan abin da ya kira labaran karya da ya ce Samira ta wallafa dangane da batun cinikin makamai. Cewar wani dan kasuwar ya karbi kwangilar da aka yi cin hanci a ciki da sunan dan shugaban kasar. Tuni dai da Samira ta kwashe sama da kwanaki 20 a gidan kason wacce ake tsare da ita tun 10 ga watan Yuni.