1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta daure Olisa Metuh shekaru bakwai

Abdullahi Tanko Bala
February 25, 2020

Wata kotu a Najeriya ta yanke wa tsohon kakakin babbar jam'iyyar adawa ta PDP daurin shekaru bakwai a gidan yari bayan samun sa da laifin cin hanci da kuma safarar kudaden haramun.

https://p.dw.com/p/3YPsx
Gebäude des obersten Gerichtshofs Nigerias in Abuja
Hoto: U.A. Idris

Mai shari'a Okon Abang na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya tabbatar da hukuncin akan Olisa Metuh bisa laifuka bakwai da hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta tuhume shi da su.

An tuhumi Olisa Metuh da karbar tsabar kudi Naira mliyan 400 ta hanyoyin da basu kamata ba daga hannun mai baiwa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan shawara kan tsaron kasa Sambo Dasuki.

Dasuki wanda shima ake tuhumarsa a wata shari'ar ta daban ana zarginsa da karkatar da akalar kudi Dala biliyan biyu na kudin sayen makamai domin yaki da Boko Haram.