Kotu ta dage zaben gwamna a Adamawa | Labarai | DW | 21.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta dage zaben gwamna a Adamawa

Wata babbar kotu da ke Yola a jihar Adamawa ta Najeriya, ta dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta sake zabe a wuraren da ba a kammala ba kamar yadda hukumar ta shirya yi a ranar Asabar har sai abin da hali ya yi.

Matakin kotun ya biyo bayan karar da dan takarar gwamna a jam’iyyar MRDD ya shigar kotun, inda yake kalubalantar hukumar ta zabe da rashin sanya alamar jam’iyyar tasa a takardar zaben gwamna da aka yi a ranar tara ga watan nan na Maris kamar yadda wakiliyarmu a Adamawa Fati Muhammad ta sheda wa DW.

Barista Aji Kamale masanin shari'a ne da ya leka kotun da ta zauna a Yola fadar gwamnatin jihar ta Adamawa ya bayyana cewa dakatar da zaben da aka shirya a ranar Asabar ya biyo bayan cewa dan takarar jam'iyyar ta MRDD ya ce ba a sanya alamar jam'iyyarsa ba a takardar zabe. Yayin da ita kuwa hukumar zabe ta ce jam'iyyar ba ta cika sharudan shiga zaben ba.