Kone-kone a kusa da ofishin INEC na Akwa Ibom | Labarai | DW | 12.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kone-kone a kusa da ofishin INEC na Akwa Ibom

Ya zuwa yanzu rahotanni da suke shigo mana sun nunar da cewa an samu wasu matasa a jihar Akwa Ibom da suka sanya wa hukumar zabe wuta.

Cikin tashe-tashen hankula da aka samu a zaben gwamnoni a Najeriya har sau 66 a cewar hukumar zabe ta INEC mafi yawa a jihar Rivers mai arzikin mai a kudu maso kudancin kasar.

Ya zuwa yanzu rahotanni da suke shigo mana sun nunar da cewa an samu wasu matasa a jihar Akwa Ibom da suka sanya wa hukumar zabe wuta saboda zargin cewa ana so a yi wa jam'iyyarsu ta APC magudi kamar yadda shedar gani da ido ya bayyanawa DW bisa sharadin kada a bayyana sunansa.

A cewar hukumar INEC baki dayan zaben an samu nasara duk da irin tashe-tashen hankulan da aka fiskanta a wasu sassan kasar.

Da yake magana da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP mai magana da yawun hukumar ta INEC Kayode Idowu ya ce ba zai bayyana adadin mutanen da lamarin ya shafa ba ya zuwa yanzu. 

A jihar Rivers ita kadai an sami tashe-tashen hankula 16 yayin da sauran 50 suka watsu a wasu sassan kasar.