Komawa gida cikin dari-dari a Borno | Siyasa | DW | 22.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Komawa gida cikin dari-dari a Borno

Daruruwan mutane sun shiga fargaba bayan da rundunar sojoji ta sake kwashe wasu al’ummomin Sabongari zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Damboa mai nisan kilomita 70 daga Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno.

Nigeria | Flüchtlingslager in Pulko (Getty Images/AFP/S. Heunis)

Nan ma wasu 'yan gudun hijira ne gaban dakunan wucin gadi a garin Pulka jihar Borno

Tun daga ranar Litinin da ta gabata ne dai rundunar sojojin Najeriya suka tara mutanen garin Sabongari da kewaye tare da sanar da su cewa za a kwashe su zuwa wasu sansanonin ‘yan gudun hijira da ba su bayyana ba.

Daga nan ne mutanen yankin cikinsu ya duri ruwa inda wasu tun a cikin daren Talata suka fara tserewa zuwa wasu yankuna saboda ba su san manufar matakin sojojin na kwashe su daga garuruwansu ba, ga kuma da yawansu ba sa son zaman sansanonin ‘yan gudun hijira.

Malam Haruna Sabongari wani ne da ya bi jeji tare da abokansa inda suka yi dace suka samu kansu a Maiduguri, ya ce mutanen da aka kai sansanin an ajiye su ba abinci sun kai azumi ruwa kawai aka ba su.

Nigeria | Flüchtlingslager in Pulko (Getty Images/AFP/S. Heunis)

Rayuwar hijira cike take da kalubale

Yanzu haka daruruwan mutane da aka kwaso daga Sabongari na zube a sansanonin ‘yan gudun hijira ba tare da wurin zama ko kuma abin da za su ci ba.

Wani matashi da ya ce sunansa Isa wanda shi ma ya zabi gudowa Maiduguri maimakon jira akai shi sansanin ‘yan gudun hijira ya ce gudun sake fadawa wahala ya sa suka gudu.

Al’ummar yankin dai sun fara yin kiraye-kirayen ga shugaban kasa da ya cire manyan hafsoshin tsaro matukar ana son magance matsalar tsaro da ta addabi yankin kamar yadda Malam Abubakar Adamu ya bayyana.

Ko a kwanakin baya ma dai sojojin sun kwashe wasu al'ummomi a Jakana da ke kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri inda daga baya aka mayar da su bisa dalilai da sojojin  suka bayyana da cewa suna aikin kakkabe mayakan Boko Haram a yankunan ne.

Sauti da bidiyo akan labarin