1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin warware rikicin Siriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 27, 2017

Jagoran bangaren 'yan adawar Siriya a tattaunawar sulhu da ake yi a birnin Geneva Nasr al-Hariri ya ce yana fatan tattaunawar da za su yi da jami'an kasar Rasha a gefen taron na Geneva, ta yi tasiri ga gwamnatin Assad.

https://p.dw.com/p/2YLtZ
Nasr al-Hariri jagoran 'yan adawar Siriya a tattaunawar Geneva
Nasr al-Hariri jagoran 'yan adawar Siriya a tattaunawar GenevaHoto: picture alliance/AP Photo/M. Trezzini

Al-Hariri  yabayyana hakan ne ga manema labarai jim kadan bayan tattaunawar da suka yi da babban jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Siriyan Staffan de Mistura a birnin na Geneva, inda ya ce suna fatan tattaunawarsu da mahukuntan Rasha ta taimaka wajen sanya wakilan gwamnatin Siriyan su shiga cikin tattaunawa domin warware rikicin kasar ta hanyar kafa gwamnatin rikon kwarya. A hannu guda kuma 'yan adawar na Siriya sun zargi Moscow da saba tanade-tanaden yarjejeniyar tsagaita wuta a Siriyan sakamakon sabon harin da jiragen yakin da ake zargin na gwamnati ne ko kuma na Rashan suka kai a birnin Idlib. Koda a ranar Jumma'ar makon da ya gabata ma dai an kai wani harin kunar bakin wake a kasar ta Siriya, a dai-dai lokacin da aka fara tattaunawar ta Geneva karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.