Kokarin shayo kan matsala a Ukraine | Labarai | DW | 22.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin shayo kan matsala a Ukraine

Shugaban Ukraine, ya gana da takwaransa na Belarus a Kiev a wannan Litinin din, sannan daga bisani da shugaban Kazakhstan Noursoultan Nazarbaïev.

Sai dai ana yi wa wannan ganawa ta shughaban na Ukraine Petro Porochenko da wadannan shugabanni ganin tamkar wani mataki na sanya tazara tsakaninsu da Rasha duk kuwa da cewa ana yi musu kallon na kusa da ita. Sai dai a hannu daya kuma ana shirye-shiryen wani sabon zaman tattaunawa tsakanin bangaren gwamnatin ta Kiev da ta 'yan awaren gabashin kasar masu goyon bayan Rasha, wanda zai gudana a birnin Minsk na kasar Belarus. Kawo yanzu dai bangarorin da ke gaba da juna ba su samu jituwa kan ranar da ta dace a soma tattaunawar ba.

Shugaban Belarus Alexandre Loukachenko, ya ce a shirye yake ya taimaka wa Ukraine na ganin ta samu sassauta wannan rikici da ke ci gaba da hallaka dumbun rayuka a gabashin kasar.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal