1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin manya na cimma burin hada kan Afirka

October 26, 2018

A kokarin hadewar Afirka nan da shekara ta 2063, shugaban kungiyar Tarrayar Afirka ta AU, Musa Alfaki, ya ziyarci Najeriya inda ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari.

https://p.dw.com/p/37GAK
Ähtiopien 29. African Union Summit in Addis Abeba
Zauren taron neman hadin kan kasashen nahiyar AfirkaHoto: picture-alliance/abaca/M. W. Hailu

Wani babban abin da ke gaban Tarrayar Afirka ayanzu shi ne tabbatar da cimma burin nan na Agenda 2063 da ya tanadi kai wa ga tabbatar da hadewar kasashe 54 na nahiyar, da zaman lafiya, sai kuma da uwa-uba habaka tattalin arziki da ya hada da kasuwanci tsakanin al’ummar nahiyar sama da miliyan dubu daya.

Nan da shekaru biyu ne dai kungiyar Tarrayar Afirka ke fatan duk wani yaki zai kare a nahiyar sannan kuma ciniki zai bude a tsakanin juna. To sai dai kuma daga dukkan alamu kungiyar ta AU na fuskantar turjiya daga kasashe kamar Najeriya, da ke kallon sannu-sannu kwana nesa.

Äthiopien Moussa Faki Kommissionsvorsitzender Afrikanische Union (AU)
Shugaban kungiyar AU, Moussa Faki Hoto: Getty Images/AFP/S. Maina

Kokarin sauyin ra’ayin dai ne ake ta’allakawa da wata ziyara ta kwanaki biyu a bangaren shugaban kungiyar ta Afirka, Musa Alfaki da ya share kwanaki biyu kuma ya gana da kusan kowa a  cikin manyan kasar, ciki kuwa har da shi kansa shugaban kasar Muhammadu Buhari.

 

To sai dai ko ma ya zuwa ina Alfakin ke fatan kaiwa da nufin sauyin matsayin mahukuntan, wadanda har yanzu ke kan dokin na ki game da batun kasuwa marar shinge a nahiyar dai; ga hukumomin Najeriya akwai bukatar sauyin tsari ga daukacin nahiyar kafin iya cimma wani abin a zo a gani ga kasashe na nahiyar.

Mahukunta cikin Najeriyar dai sun kafa kwamiti da nufin nazarin yiwuwar rattaba hannu a cikin yarjejeniyar ciniki mara shinge a nahiyar bayan korafin masu kwadagon da ke mata kallon damar kare aiki cikin kasar.

Abin jira a gani dai na zaman yadda za ta iya kayawa a tsakanin nahiyar da ke neman zaman daya; da kuma kasashe irin su Najeriyar da ke tsoron amfani da kasashen na Afirka wajen mamaya ga kasuwar cikin gidan kasar mai tasiri.