Kokarin magance matsalolin ilimi a Jamhuriyar Nijar | BATUTUWA | DW | 25.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Kokarin magance matsalolin ilimi a Jamhuriyar Nijar

Nijar ta karbi taron kungiyar CAMES mai kula da ilimi mai zurfi a kasashen nahiyar Afirka inda aka yi bitar matsalolin jami'o'in Afirka da hanyoyin magancesu a yayin da ilimin jami'oi a kasar ke fuskantar koma baya.

Nijar ta karbi taron kungiyar CAMES da ke zama wata majalisar koli mai kula da ilimi mai zurfi a kasashen nahiyar Afirka inda aka yi bitar matsalolin jami'o'in Afirka da hanyoyin magancesu a yayin da ilimin jami'oi a kasar ke fuskantar koma baya. Jami'ar Damagaram daya daga cikin manyan jami'oin kasar takwas na fuskantar koma baya a sakamakon yaje yajen aiki da dalibai da malaman ke yawan yi, a bisa neman gwamnati ta share masu hawaye kan jerin wasu koke-kokensu, wannan matsala da ake fuskanta a jami'ar ta Damagaram na gudana ne a daidai lokacin da kasar ta karbi taron kungiyar CAMES da ke zama wata majalisar koli mai kula da ilimi mai zurfi a kasashen nahiyar Afirka. An yi bitar matsalolin jami'o'in Afirka da hanyoyin magancesu.

Boren dalibai a Jamhuriyar Nijar

Boren dalibai a Jamhuriyar Nijar

Yanzu haka dai daukar darasi a jami'ar Damagaram ya kasance abun da babu tabbas biyo bayan wata yarjejeniya da aka sanyawa hannu a tsakanin kungiyoyin malaman da gwamnati duk da wa'adin watanni shida da aka dauka, gwamnatin kasar ta yi kasa a gwiwa wajen cika alkawarin abinda ya sa daliban jami'ar daukan matakin hawa dokin na ki kan tayin da gwamnati ta yi musu biyo bayan ganawarsu da ministan ilimi mai zurfi don shawo kan matsalar daliban.


Tsayawar karatu cak ko kuma tafiyar hawainiya a watanni kalilan da komawar dalibai a cewar shugaban kungiyar iyayen dalibai ko kadan bai dace ba. A yanzu haka daliban sun kaurace wa  jami'ar sakamakon wadannan matsaloli musaman yajin aikin kwararun malamai.A daidai lokacin da jami'ar ke cikin wannan matsala kungiyoyi da dama na dalibai daga na makarantun sakandare zuwa da share fagen zuwa jami'a da kuma na makarantun koyon sana'o'in hannu duk sun shiga yajin kin daukan darasi daga wadanda suka
shiga na kwanaki 2 sai zuwa 3
 

Sauti da bidiyo akan labarin