1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jihohin Najeriya sun kaddamar da yaki kan 'yan fashi

Ramatu Garba Baba
February 6, 2020

Jihohin arewa da wasu na Kudu maso yammancin Najeriya sun shiga aikin samar da isashen tsaro a yayin da gwamnati ke kara kaimi wajen magance matsalar da ta hana zaman lafiya a kasar.

https://p.dw.com/p/3XLpV
Cartoon - Air shuttle Abuja-Kaduna
Hoto: DW

Tun bayan da matsalar tsaro ta soma kamari a Najeriya, jihohin kasar suka fara sanar da sabbin matakai da suke ganin za su taimaka a yakar masu tayar da kayar baya da ke yawan kai hare-hare da sace jama'a suna neman kudin fansa. Bayan shirin Amotekun na wasu jihohi hudu a yankin Kudu maso yammancin Najeriya, a jihar Kaduna ma an samar da shiri mai taken ''Shege ka Fasa'' Rundunar za ta yaki 'yan fashi tare da tabbatar da zaman lafiya.