Kokarin dawo da tagomashin PDP a Najeriya | Siyasa | DW | 08.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kokarin dawo da tagomashin PDP a Najeriya

A kokarin sake farfado da jam'iyyar PDP a Najeriya, jam'iyyar ta gudanar da wani taro a Abuja. Hakan dai na cikin shirin babban taron kasa ne da kuma sulhuntawa 'ya'yan jam'iyyar da ma zawarcin wasu da suka sauya sheka.

Jiga-jigan jam'iyyar ta PDP ne dai suka hadu a karon farko a wannan yunkuri na sake farfado da jamiyyar don taka rawa a matsayinta na babbar  jam'iyyar adawa, da ma fuskantar babban zaben shekara ta 2019, wanda take ikirarin sake karbe madafun ikon Najeriyar da ya subule mata a zaben 2015. Sun dai ambato abubuwa da suke ganin alamu ne na haske ga sabuwar tafiyar da suka ja damara, abin da ya sanya kara kaimi a fannin sasantawa da wadanda aka batawa rai, gami da amsa cewar sun koyi darasi daga abubuwan da suka faru a baya, abinda ya sanya fara samun dawowar wasu cikin jamiyyar. Tsohon gwamnan jihar Kano malam Ibrahim Shekaru, shi ne wakili a kwamitin shirya babban taron jamiyyar. Ya ce:

''Wannan shi ne babban taro da jam'iyyar PDP ta kira tun bayan da aka warware matsalar rikicin cikin gida, kuma ya nuna cewa jam'iyyar tana nan daram. An ga sunayen mutanen da ake ta rade-raden wane ya tafi, wane baya nan. Jamiyyar PDP yanzu za ta dau sabon harami’’

Plakat Nigeria Präsidentenwahlkampf (DW/U.Haussa)

Ofishin PDP na kasa da ke Abuja

Duk wani kokari da ma tarurruka da jam'iyyar ta PDP ke yi a yanzu, batu ne na fuskantar zaben 2019 da tuni ake jan daga a tsakanin manyan jam'iyyun Najeriyar biyu na PDP da APC da ke mulki, inda ta bayyana  cewa daga yankin arewacin Najeriyar ne za su fidda ‘yan takarasu. To sai dai shirya wa zabe a kurarren lokaci lamari ne da ke sanya ayar tambaya kan tasirinsa.  

Sai dai duk da nasarar da jamiyyar ta PDP ke murnar samu, har yanzu akwai rigingimu da ke kunno kai a rassanta na wasu jihohin kasar, abin da ke sanya tambayar anya ba suna kitso ba ne da sauran kwarkwata, musamman ganin cewa ba su kai ga jawo Sanata Ali Modu Sherrif  da aka fafata da shi a kotu ba?