Kokarin dakile mamayar ′yan IS a Kobani | Labarai | DW | 04.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin dakile mamayar 'yan IS a Kobani

Sojin Kurdawan Siriya tare da tallafin hare-heren sojin Amirka sun samu nasarar dakile yunkurin 'yan IS na kame yankin Kobani da ke kan iyakar Siriya da Turkiya.

Masu aiko da rahotanni suka ce wannan hari na hadin gwiwa ya yi sanadiyyar rasuwar 'yan IS din ko da dai shaidun gani da ido sun ce 'yan IS din sun nuna turjiya sosai lokacin da aka yi dauki ba dadin da su.

Hukumar da ke sanya idanu kan kare hakkin bani adama ta Siriya wato Siriya Observatory for Human Rights ta ce 'yan IS biyar sun rasu a farmakin na Kobani yayin da wasu sama da talatin suka rasu a kusa da garin Shadadi da ke arewa maso gabashin kasar ta Siriya.

Samun nasara ta dakile kokarin 'yan IS din na kai wa ga kame Kobani dai na zuwa ne dai dai lokacin Kurdawa ke ci gaba da kiran ganin an matsa lamba wajen ganin an kawar da su daga yankin baki daya da ma dakile duk wani yankuri da suke na mallake sauran yankunan da ke Iraki da Siriya da 'yan IS din ke son yi.