1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

ICC: Ko za a hukunta Joseph Rao Kony?

September 11, 2025

An fara zaman sauraron karar Joseph Kony da aka shigar a gaban Kotun Hukunta Masu Aikata Muggan Laifuka ta Kasa da Kasa da ke birnin The Hague.

https://p.dw.com/p/50MNU
Yuganda | Joseph Rao Kony | LRA | ICC
Jagoran 'yan tawayen LRA Joseph Rao KonyHoto: Stuart Price/epa/dpa/picture alliance

An haifi Joseph Rao Kony a kauyen Odek da ke Arewacin Yuganda, jagoran 'yan tawayen da mabiyansa suka bayyana a matsayin mai bayar da bushara a lokacin da aka kama shi, kotun ICC ta bayyana shi a matsayin babban kwamandan Lord's Resistance Army (LRA).

Masu gabatar da kara na kotun ICC, sun gabatar da tuhume-tuhume guda 39 da suka hada da laifukan yaki da cin-zarafin dan Adam a kan jagoran yakin Yuganda Joseph Kony.

Wadanne laifuka Kony ya aikata?

"Haryanzu ana ci gaba da jin radadin mumunan tashin hankalin da ya jefa mutane a ciki, wadanda suka tsira na ci gaba da murmurewa daga tabon da ya girgiza ruhinsu da gangar jikinsu. Sai dai kokarin ICC na ganin an kama  Joseph Kony ya ci tura." A cewar mataimakin mai gabatar da kara a kotun ta ICC Mame Mandiaye Niang.

Niederlande Den Haag 2021 | Sitz des Internationalen Strafgerichtshofs
Kotun Hukunta Masu Aikata Laifukan Yaki ta Kasa da Kasa ICCHoto: Peter Dejong/AP Photo/dpa/picture alliance

A cewar ICC kungiyar 'yan tawayen LRA, sun aikata laifuka dabam-dabam da suka hada da kisan kai da fyade da shigar da yara aikin soja da kuma musgunawa fararen hula.

Dubban mutane sun rasa matsugunnensu

Fiye da mutane miliyan daya da dubu 900 sun rasa matsugunansu, an sace kimanin yara dubu 20 daga Yuganda an kuma kashe kimanin fararen hula 600 a hare-haren da kungiyar ta aitawar tsakanin daya ga Yulin 2002 zuwa 31 ga watan Disamba 2005 a arewacin Yuganda.

Sudan | Lords Resistance Army | Yuganda
'Yan tawayen LRA sun halaka mutane da damaHoto: AFP/Getty Images

Sai dai kungiyar LRA ta fara kai hare-hare a karshen shekarun 1990 a cewar kungiyar Human Rights Watch. Wani rahoton kungiyar a 2012 ya yi zargin Kony na rayuwa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sai dai salon kungiyar na iya zama dila sarkin dabara ya yi tasirin gaske.

Mai yake hana ICC yanke hukunci?

Manazarta na ganin rashin karfin iko daga kotun hukunta manyan laifuka, na haifar da tsaiko wajen kama shi. Kamar yadda Farfesa Kristof Titeca na jami'ar Antwerp da ke kasar Belgium ke cewa."Babban raunin Kotun Hukunta Masu Aikata Muggan Laifuka ta Kasa da Kasa a halin yanzu shi ne, ba ta da ikon kama wanda da take zargida kuma wadanda aka ba su sammaci."

A 2022 wani tsohon dan tawayen LRA Michel Mbilifouko ya shaida wa DW cewa, Kony na yankin Darfur na Sudan kuma yana ci gaba da ba da umarni ga mayakansa.

Kony na daya daga cikin mutane 10 da suka kasa shiga hannu, tun bayan bayar da sammacin kama shi a shekara ta 2005. Amurka ta yi tayin bayar da dala miliyan biyar, ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su kai ga kama shi.