Majalisar Ɗinkin Duniya ta karɓi rahoton laifukan yaƙi da Joseph Kony ya tafka
June 7, 2012
Talla
Rahoton dai ya ce a cikin shekaru ukun da su ka gabata ƙungiyar ta Joseph Kony ɗan asalin ƙasar Uganda wanda kuma ke wasan ɓuya da mahukunta, ta sace dubun-dubatar yara ƙanana inda su ka tilastawa maza daga cikinsu ɗaukar makamai yayin da su ka rinƙa lalata da matan.
Ƙunshin rahoton ya kuma ce Kony da jama'arsa waɗanda ake nema ruwa a jallo bisa zarginsu da aikata laifukan yaƙi sun aikata laifukan ne galibi a Jamhuriyar Demokraɗiyar Kongo da Sudan ta Kudu da kuma Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Umaru Aliyu