Kiran gudanar da sahihin zabe a Najeriya | Labarai | DW | 28.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kiran gudanar da sahihin zabe a Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna bukatar gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majalisun dokoki da na dattawan Najeriya cikin 'yanci da kuma walwala.

Al'ummar tarayyar Najeriya na tantance katunansu na zabe kafin su kada kuri'a da nufin zaben shugaban kasa da kuma 'yan majalisar wakilai da na dattawa. Kimanin mutane miliyan 57 ne suka cancanci samun katin kada kuri'a na din-din-din a wannan kasa da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka. Sai dai kuma tuni Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a gudanar da zaben ba tare da tashin hankali ko murdiya ba.

Tarayyar ta Najeriya ta yi kaurin suna a fannin tashe-tashen hankula a lokaci zabe da kuma bayan bayyana sakamakon zaben. Ko da a zaben 2011 fiye da mutane 1000 ne suka rasa rayukansu a rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan jam'iyyar PDP mai mulki da kuma na 'yan adawa. Sai dai kuma a wannan karon dukkanin alamu sun nunar da cewa 'yan takarar PDP Goodluck Jonathan da kuma na APC mai adawa Muhammadu Buhari na tafiya kafada da kafada a yawan magoya baya.

Tuni ma dai shugaba Jonathan ya ja hankali kan wajibin kauce ma tunzura jama'a ga haddasa rikici

"Babu wani buri na siyasa da ya ke bayar da damar haddasa tashin hankali ko kuma zubar da jinin al'umma. Ina sake jaddada aniyata ta daukan duk matakan da suka wajaba domin a gudanar da zaben nan cikin kwanciyar hankali da lumana, tare da samar da duk abubuwan da ake bukata kamar yadda dokokin kasar nan suka tanada. Bari in sake bayyana muku cewa a matsayi na na shugaban kasa, nauyi ya ratayamin a wuya na kare rayuka da kuma dukiyoyin al'umma."