Kayan agaji su fara isa ga ′yan gudun hijira a Turkiya | Labarai | DW | 25.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kayan agaji su fara isa ga 'yan gudun hijira a Turkiya

Kayan agajin shi ne rukunin farko da ya isa Turkiya domin ba wa 'yan gudun hijirar Kurdawan Siriya da ke tserewa daga ta'asar kungiyar IS.

Wani jirgin sama dauke da kayan agaji na farko daga hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ya sauka a Turkiya yayin da dubu dubatar 'yan gudun hijira daga Siriya da ke tserewa daga tashe-tashen hankula, ke ci gaba da tsallake kan iyaka zuwa Turkiya. Yaqoob Muhammad shi ne babban jami'in kula da jigilar kayayyakin agaji na hukumar kula da 'yan gudun hijira ya yi karin haske.

"Wannan na daga cikin jerin kayayyakin agaji da za mu yi jigilarsu ta sama daga birnin Amman. A cikin kwanaki masu zuwa jirgin sama na gaba zai iso da kayan. Muna sa ran isowar jirage shida daga Amman sannan daya daga birnin Copenhagen."

Jami'ai sun ce mayaka IS sun mayar da hankali a kan kwace kudancin yankin Kobani, abin da ya kara yawan mutanen da ke tserewa daga yankin. Yanzu dai mutane fiye da 100,000 akasari Kurdawa suka tsere daga garuruwa da kuma kauyuka da ke kusa zuwa Turkiya.