1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Mahara sun halaka mutum 13

May 21, 2019

'Yan bindiga sun halaka mutane 13 a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya. An kai harin ne a lokacin da manoma suka bazama gonakinsu bayan samun saukar ruwan sama a safiyar wannan Talata inda maharan suka bude masu wuta.

https://p.dw.com/p/3Iqt8
Nigeria Viehdiebstähle in ländlichen Regionen
Hoto: DW/Katrin Gänsler

An kai harin ne a garin 'Yar Gamji da ke karamar Hukumar Batsari a jihar ta Katsina.  Wani ganau ya shedawa wakilinmu Yusuf Ibrahim Jargaba cewa,  lamarin ya faru ne bayan saukar ruwan sama a yankin, inda manoma suka bazama dan yin aiki a gonakinsu kuma ba zato ba tsanmani maharan suka bude musu wuta.

Jahar Katsina da ke makwabtaka da jahar Zamfara ta fada cikin yanayi na rashin tsaro a baya-bayan nan bayan da matsalar sace mutane da yin garkuwa da su don neman kudin fansa ya kara yin kamari a sassan kauyukan Zamfaran.