Kasashen turai sun nemi karin kariya ga yan jarida | Labarai | DW | 06.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen turai sun nemi karin kariya ga yan jarida

Kasashen turai guda biyar sun bukaci komitin sulhu na majalisar dinkin duniya daya bullo da wani kudiri da zai kara kare yan jarida dake aiki a fagen daga.

Kasahen Burtaniya da Denmark da Faransa da Girka da Slovakia suka mika wannan kudirin doka wadda ake nema tayi Allah wadai da dukkanin hare hare kann yan jarida da kwararru da kuma jamian kafofin yada labarai dake aiyukan yada labarai a yankuna da ake rikici.

Kasashen na turai sunce dalilinsu na mika wannan kuduri shine halinda yan jarida suke ciki a kasar Iraqi.

Tun dai da Amurka ta mamaye kasar a 2003 yan jarida 88 suka rasa rayukansu a kasar ta Iraqi.