Kasashen G7 na taron koli a Jamus | Labarai | DW | 13.05.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen G7 na taron koli a Jamus

A wannan Juma'ar ake soma taron kasashen G7 inda taron zai yi nazari kan barazanar karancin abinci da duniya ke fuskanta a sakamakon yakin Rasha da Ukraine.

Taron kasashen G7 masu karfin tattalin arziki na zuwa ne a daidai lokacin da yakin Rasha da Ukraine ke ci gaba ba tare da alamun ganin bayansa ba, ana ganin yakin na barazanar haifar da matsalar karancin abinci mai muni, idan ba a dauki matakin gaggawa a shawo kanta ba. Yanzu haka kasashen duniya da dama na fama da hauhawar farashin hatsi da alkama dama man girki a sanadiyar rikicin.

Taron na shekara shekara da za a kamalla a gobe Asabar ya hada kan wakilai daga kasashen Britaniya da Kanada da Italiya da Faransa da Japan da Amirka dama Tarayyar Turai ya zuwa 'yan yankin Baltic da kuma Jamus mai masaukin baki.